Isa ga babban shafi

WHO za ta yi taron gaggawa saboda annobar Marburg a Equatorial Guinea

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta gudanar da wani taron gaggawa a ranar Talata bayan da akalla mutane tara suka mutu a kasar Equatorial Guinea sakamakon cutar Marburg.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya kenan, Tedros Adhanom Ghebreyesus, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Afirka ta Kudu, ranar Juma'a 11 ga watan Fabrairun 2022.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya kenan, Tedros Adhanom Ghebreyesus, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Afirka ta Kudu, ranar Juma'a 11 ga watan Fabrairun 2022. AP - Nardus Engelbrecht
Talla

Binciken masana lafiya ya nuna cewa, Marburg na cikin jinsin cutukan da ke kamanceceniya da cutar Ebola mai saurin yaduwa.

WHO ta ce taron na MARVAC ya kunshi wakilai daga fannin bincike, da kuma aiki don samar da alluran rigakafin cutar Marburg.

Kwayar cutar Marburg cuta ce mai hatsarin gaske wacce ke haifar da zazzabi mai tsanani, sau da yawa tare da zubar jini da kuma ciwon gabobi.

Marburg dai na daga cikin nau’in cutukan da ake kira filovirus wadanda suka kunshi kwayar cutar Ebola, wacce ta yi barna a wasu kasashe na Afirka.

A halin yanzu babu allurar rigakafi ko maganin rigakafi da aka amince da su don magance Marburg, amma ana iya tantance hanyoyin da za a iya amfani da su, gami da samfuran jini, da magunguna, in ji WHO.

Sanarwar na ranar Talata ta zo ne bayan da ministan lafiya na kasar Equatorial Guinea, Mitoha Ondo'o Ayekaba, ya sanar da cewa mutane tara ne suka mutu sakamakon cutar.

Ya ce an ayyana dokar ta baci a lardin Kie-Ntem da kuma gundumar Mongomo da ke makwabtaka da ita, tare da aiwatar da dokar kulle bayan tattaunawa da hukumar ta WHO.

Dokar kullen dai ta shafi mutane 4,325 a Kie-Ntem, in ji shi.

A makon da ya gabata ne gwamnatin kasar ta sanar da cewa tana gudanar da bincike kan wadanda ake zargin sun kamu da tsananin zazzabin tare da zubar da jini a yankin da ke kusa da kan iyakar kasashen Gabon da Kamaru a gabar tekun tsakiyar yammacin Afirka.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta WHO ta fitar a ranar Litinin ta ce baya ga mutuwar mutane tara, wasu mutane 16 a Kie-Ntem sun nuna alamun da ake zargin sun hada da zazzabi da aman jini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.