Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu a guguwar Freddy ya zarta 200

Adadin wadanda suka mutu sakamakon guguwar Freddy da ta afka wa kasashen Malawi da Mozambique sun zarta 200 ya zuwa yanzu, bayan da guguwar da masana suka yi ittifakin ita ce mafi muni da ta afka wa yankunan, ta haddasa ambaliya tare da zaftarewar  kasa, a   zuwanta na biyu a cikin kasa da makwanni 3 a nahiyar Afrika.

Yadda guguwar Freddy ta yi barna a Mozambique.
Yadda guguwar Freddy ta yi barna a Mozambique. LUSA - ANDRÉ CATUEIRA
Talla

Masu aikin ceto dai sun ce akwai yiwuwar samun karin wadanda wannan fitila’i ya halaka, a yayin da suke laluben wadanda suka yi katari da sauran numfashi a inda lamarin ya auku, duk kuwa da cewa an fara yanke kauna da hakan.

Karkkarfar guguwar ta  sake afka wa wannan yankin na kudu maso gabashin Afrika daga karshen makon da ya gabata ne, zuwanta na biyu tun bayan karshen watan Fabrairu, bayan da ta taso daga Australia, ta kuma  ratsa tekun India.

Gwamnatin Malawi ta ce akalla mutane 190 ne suka mutu, 584 suka jikkata, 37 kuma suka bace bat, a yayin da makwafciyarta Mozambiique ta sanar da mutuwar mutane 20  tare da 24 da suka ji rauni a bangarenta.

Kungiyar likitoci ta Medicins Sans Frontiere ta ce al’amarin ya yi kamari, kuma adadin wadanda ya rutsa da su  zai ci gaba da karuwa ne a kwanaki masu zuwa.

Wannan guguwar da ke ci gaba da haddasa ruwan sama da iska mai karfi ta raba mutane sama da dubu 19 da muhallansu, inda da dama ke tsugune a makarantu da majami’u.

Masana sun ce ba a cika samun irin wannan guguwa a wannan yankin ba, duba da cewa wadda aka yi kafin wanna ta auku ne a shekarar 2000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.