Isa ga babban shafi

Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamnonin jihohi 6

Hukumar zaben Najeriya ta sanar da sakamakon zaben Gwamnonin Jihohi 6 daga cikin 28 da akayi a karshen mako, inda jam’iyyar APC ta lashe jihohi 4, yayin da PDP ta lashe guda 2. 

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu. © The Guardian Nigeria
Talla

Sakamakon zaben ya nuna cewar jam’iyyar APC ta lashe jihohin Jigawa da Gombe da Ogun da kuma Kwara, yayin da PDP ta lashe jihohin Oyo da Akwa Ibom. 

Baturen zaben Jihar Ogun, Farfesa Kayode Adebowale ya sanar da Gwamna Dapo Abiodun na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya samu nasara bayan ya samu kuri’u 276,298, yayin da dan takaran PDP Ladi Adebutu ya zo na biyu da kuri’u 262,383.

Wasu daga cikin ma'aikatan hukumar zaben Najeriya  INEC
Wasu daga cikin ma'aikatan hukumar zaben Najeriya INEC AFP - PIUS UTOMI EKPEI

Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman Abdurazaq na Jam’iyar APC ya lashe zaben da kuri’u 273,424, yayin da Alhaji Abdullahi Shuaib Yaman na PDP ya zo na 2 da kuri’u 155,494. 

Gwamna Seyi Makinde na PDP ya lashe zaben Gwamnan jihar Oyo da kuri’u 563,756, yayin da abokin karawar san a APC Teslim Folarin ya samu kuri’u 256,685. 

A Jihar Gombe, Gwamna Inuwa Yahya ya sake lashe kujerarsa da kuri’u 342,821, yayin da abokin takararsa Muhammad Jibir Barde ya zo na 2 da kuri’u 233,131. 

Mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi na Jam’iyyar APC ya lashe zaben gwamnan jihar da kuri’u 618,449, yayin da Mustapha Sule lamido na Jam’iyyar PDP ya zo na 2 da kuri’u 368,726. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.