Isa ga babban shafi

Kotun Algeria ta daure fitaccen dan jaridar kasar shekaru 3 a gidan yari

Wata kotu a Algeria ta yanke hukuncin daurin shekaru uku ga fitaccen dan jaridar kasar Ihsane El Kadi, bisa samunsa da laifin karbar tallafin kudade daga kasashen waje don gudanar da harkokin kasuwancin sa, hukuncin da tuni kungiyoyin kare hakkin dan adam su ka yi tir da shi. 

Dan jaridar Algeria Ihsane El Kadi.
Dan jaridar Algeria Ihsane El Kadi. Youtube
Talla

El Kadi, wanda daya ne daga cikin shugabannin kafafen yada labarai masu zaman kansu a kasar da ke arewacin Afirka, hukuncin daurin shekaru biyar kotun ta yanke ma sa duk da cewa biyu daga ciki daurin talala ne. 

Kotun ta kuma bayar da umarnin rusa ginin kamfanin jaridar Interface Medias, tare da kwace kadarorinsa. 

Haka zalika kotun ta kuma ci tarar kamfanin dinari miliyan 10 kwatankwacin dala dubu 73 da dari 5, yayin da shi kansa El Kadi ya biya tarar dinari dubu dari 7. 

Lauyan sa dan jaridar Abdelghani Badi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewa tawagar lauyoyin sa za su daukaka kara don kalubalantar hukuncin. 

Hukuncin dai ya haifar da cece-kuce daga kungiyoyin kare hakkin dan adam inda wani mai shirya fina-finai a kasar Bachir Derrais, ya ce abin takaici ne yadda ake cin zarafin bangarorin yada labarai da ita kanta dimukaradiyar kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.