Isa ga babban shafi

Algeria za ta tsaurara dokokin takaita 'yancin kafafen yada labarai

Majalisar dokokin Algeria na gaf da amincewa da sabuwar dokar da za ta takaita ‘yancin ‘yan jarida a kasar, ta hanyar tsaurara ka’idojin mallakar kafafen yada labarai da kuma hana ‘yan jarida bai wa majiyoyinsu kariya.

Wasu 'yan Algeria yayin duba wasu jaridu a Algiers babban birnin kasar.
Wasu 'yan Algeria yayin duba wasu jaridu a Algiers babban birnin kasar. © Reuters/Louafi Larbi
Talla

A ranar 28 ga watan Maris majalisar wakilan Algerian ta amince da karbar kudirin dokar, wanda ake sa ran za ta kada kuri’a kansa a ranar Alhamis.

Idan har aka amince da dokar, za ta haramta wa kafafen yada labara a kasar samun kudade ko karbar taimako daga kasashen waje, kuma duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar da shi gaban kotu, gami da tarar kusan dala 15,000.

Wani rahoton kungiyar kare ‘yan jaridu na kasa ta kasa RSF, ya ce a yanzu haka Algeria ce kasa ta 134 daga cikin 180 da ke baiwa ‘yan jaridar damar gudanar ayyukansu  ba tare da tsangwama ba.

A baya bayan nan, wata kotu a Algiers babban birnin kasar ta yanke hukuncin daurin shekaru uku kan wani fitacccenn dan jarida Ihsan El kadi, bayan samunsa da laifin karbar taimakon gudanar da ayyukansa daga kasashen ketare, matakin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka yi tur da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.