Kotun ta samu kararraki shida da ke kalubalantar sakamakon zaben Oyo
Kotun sauraren kararrakin zabe a jihar Oyo da ke Najeriya ta karbi kararraki biyu dangane da zaben gwamna da hudu na zaben ‘yan majalisar dokoki.Sakataren kotun, Ibrahim Sada ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar litinin a Ibadan.
Wallafawa ranar:
Ibrahim Sada ya ce karar farko na adawa da sakamakon zaben gwamna, jam’iyyar Allied People’s Movement (APM) da dan takararta, Adeniran Oluwaseyi ne suka shigar da karar, yayin da Action Alliance (AA) da dan takararta, Babatunde Ajala suka shigar da kara ta biyu.
Sakataren ya ce an shigar da karar ne a kan sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta yi na bayyana Gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga Maris.
Ya ci gaba da cewa, jam’iyyar PDP da dan takararta na mazabar jihar Orelope, Olowokere Adewale ne suka shigar da karar majalisar dokokin jihar.
Ibrahim Sada ya ce sauran wadanda suka shigar da kara sun hada da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta na mazabar Ogbomoso ta Kudu, Adegoke Ayodeji; New Nigeria People’s Party (NNPP) da dan takararta na mazabar Ogbomoso ta Kudu, Adeniyi Oluwaseun.
Har ila yau, an samu wata takardar koke daga jam’iyyar PDP da dan takararta na mazabar Saki ta Yamma, Okedoyin Julius, na kalubalantar sakamakon zaben majalisar dokokin jihar, in ji sakataren.
Ya ce wa’adin kwanaki 21 da doka ta kayyade na shigar da kararrakin wadanda ba su ji ba basu gani ba ya ci tura, ya kara da cewa ba za a sake shigar da wata sabuwar kara ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu