Isa ga babban shafi

Jagoran 'yan adawan Saliyo na karkare yakin neman zabensa

A yayin da aka shiga ranakun karshe na yakin neman zaben shugaban kasar Saliyo, jagoran ‘yan adawa, Samura Kamara ya gudanar da gagarumin gangami a kauykan da ke kusa da babban birnin kasar. 

Samura Kamara, jagoran 'yan adawa a Saliyo.
Samura Kamara, jagoran 'yan adawa a Saliyo. AP - Craig Ruttle
Talla

Dandazon magoya bayansa sun yi ta yin sowa cikin murna a yayin gudanar da yakin neman zaben Kamara wanda ya zo na biyo a zaben da aka yi a shekarar 2018. 

Kamara ya ce, babban burinsa shi ne ziyartar daukacin kabilun da ke fadin kasar a yayin yakin neman zaben, yana mai jan hankulan jama’a  da su guji masu neman raba kawunansu ta fuskar kabilanci, inda ya ce gaba dayansu ‘yan kasa guda ne masu ‘yanci iri daya. 

A ranar Asabar mai zuwa ne jama’ar Saliyo za su fita zuwa rumfunan zabe domin zabe kuma tuni masharhanta kan lamurran siyasa suka yi hasashen cewa, za a yin kan-kan-kan tsakanin Kamara da shugaba Julius Maada Bio kamar dai yadda ‘yan takarar biyu suka yi a zaben 2018. 

Da kyar dai shugaba Bio ya doke Kamara a zagaye na biyu na zaben wancan lokcain da tazarar da ba ta wuce kashi biyar cikin 100 ba. 

Ana bukatar dan takara ya samu kashi 55 a zagayen farko kafin ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara ba tare da zuwa zagaye na biyu ba. 

Sama da mutane miliyan uku ne suka yi rajistar kada kuri’a a zaben na karshen makon nan a Saliyo. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.