Isa ga babban shafi

Shugaban Saliyo ya zargi 'yan adawa da shirin kifar da gwamnati

Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio ya zargi jam’iyyun adawa da shirya mummunar zanga zangar da ta kaiga rasa rayuka a matsayin hanyar kifar da gwamnatin sa.

Mutane na tsarewa yayin wata zanga-zangar adawa da gwamnati, a Freetown, Saliyo, 10 ga Agusta, 2022 a wannan hoton da aka samu daga kafafen sada zumunta. Hoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters/ta hanyar REUTERS ya samu wannan hoton wani bangare ne na uku. KASHIN WAJIBI.
Mutane na tsarewa yayin wata zanga-zangar adawa da gwamnati, a Freetown, Saliyo, 10 ga Agusta, 2022 a wannan hoton da aka samu daga kafafen sada zumunta. Hoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters/ta hanyar REUTERS ya samu wannan hoton wani bangare ne na uku. KASHIN WAJIBI. via REUTERS - PICTURE OBTAINED BY REUTERS
Talla

Yayin da yake jawabi ga jama’ar kasar ta kafar talabijin, shugaban wanda tsohon Janar na soji ne, yace 'yan adawan sun dade suna kitsa tashin hankali a cikin kasar.

Tsadar rayuwa

Bio yace zanga zangar da akayi ba'an shirya ta ne saboda tsadar rayuwa ko kuma hauhawan farashi ba, saboda matsalar hauhawar farashin ta zama matsalar da ake ganin a kasashen duniya baki daya.

Shugaban yace ihuce ihucen da aka gani lokacin zanga zangar wani yunkuri ne na amfani da karfi wajen kifar da zababbiyar gwamnati wanda ya zargi ‘yayan jam’iyyar APC da PPP da kitsawa.

Shirin Juyin mulki

Bio yace wadannan 'yan siyasa sun yi amfani da masu zanga zangar wajen kawar da zaman lafiya da tsaro da kuma tsarin kasar wajen daukar nauyi da kuma bada kudade.

Jim kadan bayan jawabin Jam’iyyar adawa ta APC ta fitar da sanarwa inda ta bukaci jama’ar kasar da su mutunta doka da oda, ba tare da mayar da martani akan zargin da shugaban kasar yayi akan su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.