Mutane da dama sun mutu yayin wata zanga-zanga a Saliyo
Jami’an ‘yan sanda biyu ne aka kashe a kasar Saliyo, bayan wata zanga-zangar nuna adawa da matsalar tattalin arziki da ta barke tsakanin jami’an tsaro da matasa tare da neman shugaban kasar ya yi murabus.
Wallafawa ranar:
Hakan ta sanya mataimakin shugaban kasar Mohamed Juldeh Jalloh ya sanar da kafa dokar ta-baci a fadin kasar yayin da ya fitar da sanarwar cewa an kashe wasu daga cikin masu zanga-zangar, ciki har da wasu jami’an tsaro.
hukumomin tsaron kasar sun ce an kama masu zanga-zangar da dama, yayin da fusatattun matasa da dama suka shaidawa AFP cewa ‘yan sand ana harba musu harsasai.
Wani ma'aikacin lafiya a wani asibiti da ke Freetown ya ce mutane da dama sun jikkata.
A yankin Kissy da ke gabashin birnin, masu zanga-zangar sun jefi jami'an tsaro da duwatsu da sanduna, bayan da suka harba musu hayaki mai sa hawaye.
An dai ji masu zanga-zangar suna rera taken "Bio must go" wato suna nufin shugaba Julius Maada Bio, wanda a halin yanzu yake kasar Burtaniya a wata ziyarar sirri sai ya sauka daga shugabancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu