Isa ga babban shafi
Saliyo-Yakin basasa

Saliyo na bikin cika shekaru 20 da kawo karshen yakin basasar kasar

Dubban Al’ummar Saliyo sun gudanar da Maci da bukukuwa a babban birnin kasar Freetown don nuna farincikin su na cikar kasar shekaru 20, tun bayan kawo karshen yakin basasar da ya tasamma daidaita kasar.

Shugaba Julius Maada Bio yayin jawabi ga al'ummar kasar.
Shugaba Julius Maada Bio yayin jawabi ga al'ummar kasar. © Kelvin Lewis
Talla

An dai kawo karshen yakin basasar Saliyo tun ranar 18 ga watan Janairun 2002 lokacin da tsohon shugaban kasar Ahmed Tejan Kebbah ya sanar da kawo karshen yakin basasar kasar da ya barke a shekarar 1991 a garin Lungi.

Yakin dai da ake ganin yana samun goyon bayan wasu kasashen waje, an fara shi ne da nufin kifar da gwamnatin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, da kuma kara yawan yara kanana a aikin soja.

Sama da ‘yan gwagwarmaya 70 ne suka taru a garin Lungi don yin maci da nuna farincikin su da wanzuwar zaman lafiya a kasar, tun bayan kawo karshen yakin.

‘Yan gwagwamaryar dai sun rika wake-waken hadin kan kasa da zaman lafiya da daga tutar kasar da take rainon ingila, kuma guda daga cikin matalautan kasashen na gaba-gaba a duniya, duk da arzikin lu’ulu’un da take da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.