Isa ga babban shafi
Saliyo

Dole Saliyo ta yi koyi darasi daga fashewar tankar mai - Shugaban kasa

Shugaban Saliyo Julius Maado Bio ya bukaci jama’ar kasar da su koyi darasi daga kazamin hatsarin da aka samu na gobarar man fetur wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan 100.

Wurin da aka samu hatsarin tankar man da ya janyo mutuwar mutane kusan 100 a kasar Saliyo.
Wurin da aka samu hatsarin tankar man da ya janyo mutuwar mutane kusan 100 a kasar Saliyo. AFP - SAIDU BAH
Talla

Yayin da yake jawabi bayan komawar sa gida daga taron sauyin yanayi, shugaban yace zasu ci gaba da taimakawa wadanda hadarin ya ritsa da su.

Ma’aikatar agajin gaggawar kasar ta Saliyo tace adadin da mutanen da suka mutu sakamakon gobarar man ya kai 98, yayin da wasu 92 suka tsira.

Gobarar dai ta biyo bayan fashewar tankar man da tayi taho mu gama da wata babbar mota, a wani gidan mai dake Freetown, babban birnin kasar a daren ranar Juma’ar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.