Shugaban Saliyo Julius Maada Bio zai ziyarci unguwar da gobara ta tashi
Gwamnatin Saliyo tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan mai ya kai 98, abinda yayi sanadiyar konewar motoci tare da mutanen da dake ciki.
Wallafawa ranar:
Hukumomin kula da lafiyar kasar sun ce gawarwakin da suka tantance sakamakon hatsarin da ya faru a ranar juma’a sun kai 98, yayin da ake danganta hadarin da kama wutar da wata mota tayi sakamakon karo da motar dakon mai.
Hukumar kai daukin gaggawa ta kasar ta bakin Shugaban ta tace zai yi wuya a tattance iyalan mutanen da suka kone kurmus.
Fadar Shugaban kasar ta bayyana cewa shugaban kasa Julius Maada Biyo zai ziyarci unguwar da lamarin ya faru a yau lahadi biyo bayan bayyana kaduwar sa da hatsarin wanda ya kai ga asarar tarin rayuka .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu