Isa ga babban shafi

Saliyo ta kafa dokar bai wa Mata kashi 30 na dukkanin guraben ayyuka a kasar

Shugaba Julius Maada Bio na Saliyo ya sanya hannu kan wata sabuwar doka da ta bukaci bayar da kashi 30 na guraben ayyuka ga Mata a ilahirin ma’aikatu, bangarori da kuma sassan gwamnatin kasar, ciki kuwa har da shugabancin madafun iko kama daga na zamani da kuma sarautun gargajiya, wadanda a baya Maza kadai ke jagoranci.

Wasu Mata a Saliyo yayin murnar sabuwar dokar da ta basu damar mamaye kashi 30 na dukkanin guraben ayyyuka a kasar.
Wasu Mata a Saliyo yayin murnar sabuwar dokar da ta basu damar mamaye kashi 30 na dukkanin guraben ayyyuka a kasar. AP - Cooper Inveen
Talla

A jawabinsa lokacin sanya hannu kan sabuwar dokar wadda aka yiwa lakabi da dokar samar da daidaito tsakanin jinsi yayin bikin da ya gudana a birnin Freetown, Shugaba Maada Bio ya ayyana jiya juma’a a matsayin ranar kawo karshen nuna banbanci da hana mata gogayya da takwarorinsu maza yana mai yakinin cewa dokar za ta fara aiki nan ta ke.

Karkashin dokar na nuna cewa yanzu mata ne za su mamaye kasha 30 na kujeru 146 da Majalisar Saliyo ke da su, wadda a yanzu ake da ‘yan Majalisu mata 18 kadai ciki har da 4 mambobin jam’iyyar shugaba Bio.

A cewar shugaba Bio ya na da masaniyar cewa aiwatar da wannan doka zai zo da tarnaki musamman lura da yadda maza suka shafe tsawon shekaru suna rike da guraben, inda ya ce nauyi ne akan gwamnatinsa ta sanya idanu don ganin mata sun samu gurabe a wuraren aiki da kuma zauren Majalisar.

Karkashin dokar dai dukkanin ma’aikatar da aka samu da laifin kin mutunta tsarin na bayar da damarmakin kashi 30 ga mata za a ci tararta yuro dubu 2 da 400 kan duk mutum guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.