Isa ga babban shafi

Somalia ta bukaci ci gaba zaman dakarun Afrika a kasar zuwa nan da kwanaki 90

Somalia ta bukaci tsawaita wa’adin kammala ficewar dakarun Afrika daga kasar zuwa nan da kwanaki 90 masu zuwa don taimaka mata wajen ci gaba da yakar ‘yan ta’addan kungiyar Al-Shabaab.

Dakarun kasashen Afrika a Somalia.
Dakarun kasashen Afrika a Somalia. REUTERS - FEISAL OMAR
Talla

Wata wasika da babban mashawarcin gwamnatin Somalia kan harkokin tsaro ya aikewa Majalisar Dinkin Duniya ce ta bukaci tsawaita shirin ficewa rukuni na biyu na dakarun daga kasar, inda wasikar ke cewa ci gaba da zaman dakarun zai taimaka a yakin da ake wajen murkushe mayakan Al-Shabaab.

Kafin wannan roko dai, zuwa nan da karshen watan Satumban da muke ciki ne dakarun kasashen Afrika akalla dubu 3 za su kammala barin kasar mai fama da matsalolin tsaro.

Gwamnatin Somalia karkashin jagorancin shugaba Hassan Sheikh Mohamud, ta aza harsashin wani yunkuri da ta kira a matsayin na karshe da zai kai ga kammala kakkabe mayakan na Al-Shabaab wadanda Sojojin kasar da taimakon na ketare suka shafe fiye da shekaru 15 su na yakarsu.

A baya-bayan nan dai an ga tsagaitawar hare-haren mayakan na Al-Shabaab musamman a birnin Mogadishu fadar gwamnatin Somalia sai dai sun zafafa hare-harensu kan yankunan gefen birnin cikin har da sansanonin dakarun Sojin Afrika.

Ana dai alakanta, matakin ficewar dakarun na kasashen Afrika da tsanantar hare-haren mayakan Al-Shabaab a baya-bayan nan wanda ya kai ga kisan gomman dakarun musamman na Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.