Isa ga babban shafi

Nijar ta janye batun rufe mahakar zinare mafi girma a kasar

Majalisar mulkin sojin Nijar, wacce ta kifar da gwamnatin dimokuradiyya a karkashin jagorancin Mohamed Bazoum, ta jingine batun rufe mahakar zinari mafi girma a kasar da ke garin Tchibarakaten kusa da iyakar kasar da Aljeriya. 

Yadda mahakan zinare ke aiki a yankin Ituri da ke Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Yadda mahakan zinare ke aiki a yankin Ituri da ke Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo. AFP PHOTO / JOSE CENDON
Talla

Kafin kifar da ita daga karangar mulki, tuni gwamnatin Bazoum ta sanar da wani kudiri da ke cewa za a rufe ma’adinin saboda dalilai na tsaro. 

Gwamnatin sojin kasar dai ta ce, za a yi amfani da wannan mahakar zinare wajen samar da kudaden shiga ga Nijar, domin kara inganta tattalin arzikinta.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Oumarou Sani.

Hukumomin kasar karkashin gwamnatin Bazoum, sun yi zargin cewa, akwai wadanda ke hako zinare a yankuna da dama ba tare da sahalewar gwamnati ba, abin da ake ganin shine ke haifar da matsalolin tsaro.  

Hakan ta sanya aka kaddamar da shirin wayar da kan matasa, kan ka'idojin hako ma'adanai amma bisa sahalewar hukumomin da abun ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.