Isa ga babban shafi

An sako tsohon shugaban ma'aikatan Bongo bayan shafe kusan shekaru 4 a tsare

An sako tsohon shugaban ma’aikatan hambararren shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba daga gidan yari, bayan ya shafe kusan shekaru hudu a tsare, sakamakon fito na fito da yayi da mai dakin Bongo, Sylvia Bongo Ondimba.

An sako Laccruche Alihanga, tsohon shugaban ma’aikatan hambararren shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba daga gidan yari, bayan ya shafe kusan shekaru hudu a tsare.
An sako Laccruche Alihanga, tsohon shugaban ma’aikatan hambararren shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba daga gidan yari, bayan ya shafe kusan shekaru hudu a tsare. AFP
Talla

Laccruche Alihanga, da dan uwansa Gregory da tsohon ministan sufurin kasar Justin Ndoundangoye, wadanda aka rufe a gidan yari tun a ranar 3 ga watan Disamban shekarar 2019, an sako su ne a rana guda, amma sai dai ba a kawo karshen  shari'a su ba.

A yanzu dai daurin talala akayi musu, inda za a ci gaba da tuhumar su da laifin almubazzaranci da dukiyar al’umma.

Tun bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a ranar 30 ga Agustan da ya gabata, wanda ya kawo karshen mulkin Ali Bongo Ondimba, aka fara tuhumar mai dakin Sylvia Bongo Ondimba da laifin karkatar da kudade, inda ake tsare da ita a gidan yari na Libreville tare da Brice Laccruche Alihanga.

Mai dakin habararren shugaban Gabon, Sylvia Bongo Ondimba.
Mai dakin habararren shugaban Gabon, Sylvia Bongo Ondimba. AFP - GABRIEL BOUYS

A ranar 28 ga watan Satumban da ya gabata ne, Kotu ta fara tuhumar Sylvia Bongo kan tarin laifukan da ake tuhumarta bayan juyin mulkin Sojin da ya hambarar da kujerar mai gidanta.

Sojojin da ke mulki a Gabon dai sun zargi mukarraban hambararren shugaban da laifin sauya sakamakon zabe ciki har da mai dakin nasa wadda suka ce ta yi amfani da damar rashin lafiyarsa wajen satar makuden kudade daga lalitar gwamnatin kasa tun daga shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.