Isa ga babban shafi

Gabon ta tuhumi matar hambararren shugaban kasar da laifin karkatar da kudade

Ana tuhumar Sylvia Bongo Ondimba Valentin, ‘uwar gidan hambararren shugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba da laifukan wawaso ga dukiyar kasar, kamar yadda mai gabatar da kara ya bayyana, wata guda kenan bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

'Uwar gidan hambararren shugaban Gabon, Sylvia Bongo Ondimba.
'Uwar gidan hambararren shugaban Gabon, Sylvia Bongo Ondimba. AFP - GABRIEL BOUYS
Talla

Lauyan masu shigar da kara, Andre Patrick Roponat, na tuhumar ta da halasta wa kanta kudin haramun.

“An kama wasu ‘yan kasar guda goma sha biyu da ake tuhuma da aikata laifuka, inda wasu daga cikin su ke tsare a gidan yari. A cikin wannan yanayi ne Madame Sylvia Bongo Ondimba Valentin ta bayyana a gaban majistare a ranar 28 ga watan Satumba 2023. Ana tuhumar ta da laifin karkatar da kudade, karbar kayan sata da kuma aikata zamba, kuma wadannan laifukan sun ci karo da sashe na 116, 117, 312 da 380 na kundin laifuffuka," a cewar Andre Patrick.

Matar tsohon shugaban kasar dai an haramta fita daga Gabon, tun bayan da aka hambarar da mijinta a ranar 30 ga watan Agusta.

A lokacin da aka kifar da gwamnatin Bongo, fadar shugaban kasar ta ce Valentin tana tsare a gidanta da ke Libreville, amma lauyoyinta da ke Faransa sun ce an tsare ta ba bisa ka'ida ba.

Ali Bongo, wanda da farko aka tsare shi a Libreville bayan juyin mulkin, daga bisani gwamnatin mulkin sojin ta bashi 'yancin tafiya kasashen waje domin neman lafiyarsa.

Tuni dai aka tuhumi danta Noureddin Bongo Valentin da laifin almundahana da dukiyar al'umma tare da wasu tsoffin ministoci biyu.

Zargin tafka magudin zabe ne ya haddaa juyin mulkin

Bongo, mai shekaru 64, wanda ya mulki kasar da ke tsakiyar Afirka tun shekara ta 2009, shugabannin sojoji sun hambarar da shi, bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Sakamakon zaben da aka fitar dai ‘yan adawa sun bayyana cewa an tafka magudi a cikinsa, wadanda kuma ke zargin gwamnatinsa da cin hanci da rashawa da kuma rashin shugabanci na gari.

Ali Bongo ya hau kan karagar mulki ne lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009 bayan shafe kusan shekaru 42 yana mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.