Isa ga babban shafi

Sojojin Gabon za su kira tattaunawar kasa don samar da sabon kundin tsarin mulki

Sojojin da ke mulki a Gabon sun gabatar da jadawalin shirin tattaunawar kasa a shekara mai zuwa wanda ake sa ran ya bude hanyar samar da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Janar Brice Oligui Nguema na Gabon.
Janar Brice Oligui Nguema na Gabon. © AFP
Talla

Fitar da jadawalin na zuwa ne kasa da wata guda bayan juyin mulkin Soji a kasar ta Gabon wanda ya hambarar da kujerar Ali Bongo Odimba da ya shafe shekaru 14 ya na mulkar kasar mai albarkatun karkashin kasa, kakakin gwamnatin Sojin Raymond Ndong Sima ya shaidawa taron manema labarai a Libreville cewa zuwa nan da makon gobe za a fitar da jadawalin ga al’ummar kasar.

Ko a makon jiya Ndong Sima ya kare matakin juyin mulkin na Gabon yayin jawabin da ya gabatar gaban zaman babban zauren Majalisar Dinkin Duniya inda ya ce matakin kwace ikon da Sojoji suka yi, ya taimaka wajen dakile zubar da jini.

Jagoran mulkin Sojin na Gabon, Brice Oligui Nguema wanda aka rantsar da shi a matsayin shugaban rikon kwarya, ya sha alwashin mayar da kasar turbar demokradiyya bayan gudanar da zabe, duk da cewa bai sanar da tsawon lokacin da mulkin rikon kwaryar nasa zai dauka ba.  

A cewar Ndong Sima, za a tattara shawarwari daga sassa daban-daban na kasar gabanin fitar da sabon kundin tsarin mulkin tafiyar da kasar wanda zai gudana tsakanin watanni Aprilu zuwa Yunin shekara mai zuwa.

A cewarsa, al’ummar kasar na bukatar akalla kwanaki 45 zuwa 60 gabanin iya bayar da cikakkiyar gudunmawa yayin tattaunawar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.