Isa ga babban shafi

Sojojin Gabon sun tisa keyar matar hambararren shugaban kasar zuwa gidan yari

Kotu a Gabon ta aike da matar hambararren shugaban kasar Ali Bongo Ondimba gidan yari bayan samun ta laifukan almundahana da halasta kudin haram da kuma bayar da bayanan karya.

Mai dakin hambararren shugaban kasar Gabon, Sylvia Bongo Ondimba.
Mai dakin hambararren shugaban kasar Gabon, Sylvia Bongo Ondimba. AFP - GABRIEL BOUYS
Talla

Mai dakin tsohon shugaban, Sylvia Bongo Ondimba Valentin wadda kafin hukuncin na Jiya Laraba ta ke fuskantar daurin gida tun bayan juyin mulkin na karshen watan Agusta, sojojin da ke mulkin kasar suna kuma tuhumarta da karkatar da kudaden jama’a.

Lauyanta Francois Zimeray ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP yau Alhamis cewa tun a jiya Laraba kotun ta yi umarnin tisa keyarta zuwa gidan yari dangane da zargin na halasta kudaden haramun.

A ranar 28 ga watan Satumban da ya gabata ne, Kotu ta fara tuhumar Sylvia Bongo kan tarin laifukan da ake tuhumarta da su kasa da wata guda bayan juyin mulkin Sojin da ya hambarar da kujerar mai gidanta.

Sojojin da ke mulki a Gabon dai sun zargi mukarraban hambararren shugaban da laifin sauya sakamakon zabe ciki har da mai dakin nasa wadda suka ce ta yi amfani da damar rashin lafiyarsa wajen satar makuden kudade daga lalitar gwamnatin kasa tun daga shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.