Isa ga babban shafi

Sojojin da ke mulki a Gabon sun yi nadin mambobin majalisun dokokin kasar

Sojojin da ke mulki a Gabon sun gudanar da nadin sabbin ‘yan majalisun dokoki da sanatoci don samun damar tafiyar da sabuwar gwamnatin rikon kwarya gabanin kiran zaben da suka alkawarta yi, ko da ya ke har yanzu ba su tsayar da tsawon lokacin da za su dauka suna mulkin ba, bayan hambarar da gwamnatin Ali Bongo Ondimba.

Janar Brice Oligui Nguema, jagoran mulkin Sojin Gabon.
Janar Brice Oligui Nguema, jagoran mulkin Sojin Gabon. AFP - -
Talla

Jagoran mulkin Sojin na Gabon Janar Brice Oligui Nguema ne ya jagoranci nadin sabbin ‘yan majalisun a yau asabar, wadanda suka kunshi wakilci daga kusan dukkanin yankunan kasar.

Wannan nadi na zuwa ne bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yiwa gwamnatin shugaba Ali Bongo a ranar 30 ga watan Agusta wanda ya kawo karshen shekaru 55 da iyalan gidan Bongo suka shafe suna mulkar kasar.

Gwamnatin Sojin ta Gabon ta sha alwashin gudanar da karbabben zabe a kasar a tsakanin watan Aprilu zuwa Yunin shekarar 2024 don mayar da mulki ga fararen hula.

Kakakin gwamnatin Sojin ya karanto sunayen mutane 98 wadanda su ne za su jagorancin majalisun kasar ciki kuwa har da bangaren adawa da kuma bangaren magoya bayan hambararren shuga Ali Bongo Ondimba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.