Isa ga babban shafi

Birtaniya da Rwanda sun kulla yarjejeniya kan bakin haure duk da haramcin kotu

Birtaniya da Rwanda sun sake rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ranar Talata a wani kokarin na kaucewa hukuncin da wata kotu ta yanke na dakile manufar gwamnatin kasar mai cike da cece-kuce na tura masu neman mafaka zuwa kasar da ke gabashin Afirka.

Ministan harkokin cikin gidan Birtaniya James Cleverly da takawaransa na Rwanda Vincent Birutane yayin sanya hanu kan sabuwar yarjejeniyar mayar da masu neman mafaka Rwanda. 05/12/23
Ministan harkokin cikin gidan Birtaniya James Cleverly da takawaransa na Rwanda Vincent Birutane yayin sanya hanu kan sabuwar yarjejeniyar mayar da masu neman mafaka Rwanda. 05/12/23 AP - Ben Birchall
Talla

Ministan harkokin cikin gidan Birtaniya James Cleverly da takawaransa na Rwanda ne suka sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar mayar da masu neman mafaka  daga Birtaniya zuwa Kigali.

Hukuncin Kotun Koli

Ziyarar jam’in na Birtaniya a ranar Talata na zuwa ne wata guda bayan da Kotun Kolin Birtaniya ta yanke hukunci, da ke tabbatar da haramcin shirin kasashen na tusa keyar yan ci rani zuwa Rwanda.

Sabuwar yarjejeniyar zata tabbatar da cewar Rwanda ba ta kori masu neman mafaka zuwa kasar da watakila ke zama barazana ga rayuwarsu ko 'yancinsu ba, wanda ke zama data daga cikin manyan babatuwa da kotun ta yi la’akari da su wajen yanke hukucin.

Ministan harkokin cikin gidan Birtaniya James Cleverly da takawaransa na Rwanda Vincent Birutane yayin sanya hanu kan sabuwar yarjejeniyar mayar da masu neman mafaka Rwanda. 05/12/23
Ministan harkokin cikin gidan Birtaniya James Cleverly da takawaransa na Rwanda Vincent Birutane yayin sanya hanu kan sabuwar yarjejeniyar mayar da masu neman mafaka Rwanda. 05/12/23 AP - Ben Birchall

Kazalika za a samar da kwamitin sa ido domin baiwa mutane damar shigar da kararrakin sirri kai tsaye, da kuma kafa sabuwar hukumar daukaka kara da ta kunshi alkalai daga sassan duniya.

Wasu kashe na neman yin koyi

Shirin tura 'yanci rani zuwa Rwanda da ke zama  wani  muhimman batu ga gwamnatin Birtaniya domin rage yawan masu neman mafaka a cikin kasarta, ya kasance wani abin da wasu kasashe dake bukatar daukar irin wannan salon siyasa na Birtaniya a cikin kasashensu ke bi sau da kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.