Isa ga babban shafi

Maroko zata taimakawa Nijer- Mali da Burkina Faso ta hanyar zuba jario a cikin kasashensu

A karshen makon da ya gabata  ne,  kasar Maroko ta gudanar da wani taro na farko da kasashen Mali, Burkina Faso da jamhuriyar Nijer. Inda ta gabatrwa kasashen tayin zuba jari a cikinsu da zai taimaka wajen isar da kasshen na yankin Sahel ga gabar Tekun   Atlantique, domin taimakawa  fitar da kasashen daga kawanyar da kasshe suka yi masu wajen hanasu kaiwaga gabar Teku.

wasu mahalarta taron hukumar bayar da lamani ta duniya IMF da Bankin Duniya a  Marrakech a ranar 10 ga octobre 2023.
wasu mahalarta taron hukumar bayar da lamani ta duniya IMF da Bankin Duniya a Marrakech a ranar 10 ga octobre 2023. © Susana Vera / Reuters
Talla

Ministocin harakokin wajen kasashen 4 dai, sun gudanar da zaman taron nasu ne a Marrakech, wanda ke nuna  buda  wani sabon kawancen tattalin arziki, da siyasa tsakanin kasashen da Maroko .

“Duk wanda ya baka ruwa,  to kuwa babu shakka ya baka  rayuwa ne, in ji  ministan harakokin wajen kasar Mali  Abdoulaye Diop,  amatsayin nuna godiyar kasashen uku dake yankin Sahel, dangane da wannan tayin  ayukan bunkasa tattalin  arizikin  da  Maroko ta gabatar ma su.

Budewa kasashen na kofar isa ga gabar tekun  atalantique, ya hada ne da basu damar samun gine-ginen hanyoyi, buda masu kofofin kasuwanci da kasashen duniya: su ne alkawulan da sharifiyar masarautar ta Maroko  ta shirya, domin taimakawa abukasuwar  tattalin arzikin uku, da su ma  suka bayyana amincewarsu da tayin da Maroko ta yi masu.

Bugu da kari, ministocin sun bayyana bukatar ganin an zage dantse da wuri  wajen tunkarar wannan muhimmiyar shawara.

Don saboda baiwa kasashen yankin sahel damar kara amfana da budin na Maroko da zaikaisu ga  gabar ruwan tekun Atlantique, gine-gine da dama ne ake bukata, da suka hada da hanyoyi da kuma filayen jiragen sama  nada matukar muhimmanci a cikin shirin.

Idan kasshen Sahel sun bayyana aniyar zuba jari domin karbawa shawarar ta Maroko, za a iya cewa, yanzu ne za a shiga tunanin yadda huldar zata kasance, ministocin harakokin wajen kasashen hudu, sun cimma matsaya wajen kafa komitoci a ko wace kasa da take bukatar shiga Shirin domin shiryawa da kuma gabatar da shawarar, yadda shawarar ta Maroko zata yi aiki.

Ko ma dai me ke faruwa, ya kamata a fayyace yadda wanan shiri na tattalin arziki zai wakana, haka kuma samun kyakyawan  hadin kan diplomatique, zai taimaka wajen tabbatuwar Shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.