Isa ga babban shafi

Bankin Duniya da IMF sun bayyana aniyar mayar da hankali kan ci gaban nahiyar Afrikia

Manyan Hukumomin bayar da lamuni na duniya IMF da  Bankin duniya, sun ce yanzu za su fi mayar da hankali ne  ga lamuran da suka shafi ci gaban Nahiyar Afirka.Hukumomin sun bayyana haka ne a wani taron shekara shekara da aka buda a farkon wannan mako da muke ciki a Marakesh na Kasar Morocco. 

O Fundo Monetário Internacional mantém suas previsões de crescimento para a economia mundial em 2023.
O Fundo Monetário Internacional mantém suas previsões de crescimento para a economia mundial em 2023. AFP - FADEL SENNA
Talla

Shugabar asusun bada lamunin ta duniya uwargida Kristalina Georgieva ce, ta bayyana cimma nasarar Karni na 21 a  nahiyar ta Afirka wanda maida  hankali a kansa  ya zama wajibi. 

Manyan jijiyoyin tafiyar da tattalin arzikin na duniya Asusun IMF da Bankin duniya na gudanar da wannan ganawa ce, a karon farko cikin shekaru 50 a Nahiyar Afirka. 

Wanda a wannan karo ake tattaunawa akan abin da ya shafi yadda za’a samar da dai-daituwar lamuran tattalin arziki na duniya, batun bambance-bambance  da kuma sauyin yanayi. 

A cikin bayanan da ta wallafa, hukumar ta IMF ta cek, ta yi gwagwarmayar ganin dorewar kashi 3% na tattalin arzikin duniya a shekarar 2023 ba tare da ya sauya ba, duk kuwa da wasu alamun rauni da aka samu a yawancin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.