Yau za a fara gasar kwallon kafa ta nahiyar Afrika a Ivory Coast
A wannan asabar ake fara gasar kwallon kafa ta cin kofin nahiyar Afrika a Ivory Coast, inda mai masaukin bakin za ta barje gumi a wasan farko da Guinea Bissau.
Wallafawa ranar:
Ivory Coast, wadda ta taba lashe wannan kofin a shekarar 1993 da 2015, za ta fafata da takwararta Guinea Bissau ne a filin wasa na Alassane Ouattara mai daukar 'yan kallo dubu 60.
Za a karkare gasar ta AFCON karo na 34 da wasan karshe da za a yi a ranar 11 ga watan Fabrairu.
A ranar 27 ga watan Janairu ne za a fara wasannin matakin sili daya kwale, a kuma buga wasannin daf-da-na-kusa-da -karshe a ranar 2 ga watan Fabrairu, sai kuma wasannin kusa da karshe da za a fafata a ranar 7 ga watan Fabrairu.
Kasar Masar, wadda za a dama da ita a wannan gasa, ita ce ta fi kowace kasa cin wannan gasa, inda sau 7 tana lashe kofin, Sai kamaru mai bi mata da kofuna 5, sannan Ghana da kofuna 4 sai kuma Najeriya da ta lashe kofuna 3.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu