Isa ga babban shafi

Manyan hafsoshi a Gabon za su iya kara auren mata da yawa

Hukumomin kasar Gabon, Majalisar Ministoci ta amince da wani daftarin doka da ke bai wa manyan hafsoshi da Janar-janar soji damar auren mace fiye da daya idan sun bukaci haka. Wasu na zargin sojoji da nuna bangaranci da rashi kwarewa a bangaren aiki.

Shugaban majalisar sojin Gabon Janar Brice Oligui Nguema
Shugaban majalisar sojin Gabon Janar Brice Oligui Nguema © AFP
Talla

Daga bangaren matasa,wasu yan kasar na nuna goyo bayan su ga majalisar sojin kasar ta Gabon,inda matashi mai suna Olivier Emvo Ebang ya samar da kungiyar "Dole ne Oligui ya zauna",kungiyar da ke goyan bayan shugaban rikon kwarya da kuma wannan shawarar a madadin manyan hafsoshi.

Bikin aure a kasar Gabon
Bikin aure a kasar Gabon © Sarah Codjo

 

Sai dai wasu daga cikin Shugabanin mata na kasar ta Gabon irin su Sidonie Flore Ouwé,sabuwar dokar ba ta da kyau sosai.

A babban birnin kasar,Libreville, jama’a na fassara wannan doka ta fuskoki da dama.

 

Daurin aure
Daurin aure AFP - ATTA KENARE

A hukumance, suna auren mace ɗaya, amma a rayuwar yau da kullun, suna da mata da yawa a bayan fage. Dokar iyali ta Gabon ta ba wa namiji damar auren mata har biyar. Har yau sojoji ba su da wannan hakkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.