Isa ga babban shafi

Kenya da Haiti sun cimma yarjejeniyar dafawa juna ta bangaren aikewa da jami'an tsaro

Shugaban Kenya William Ruto ya ce Kenya da Haiti sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a jiya Juma'a don tura 'yan sanda daga kasar da ke gabashin Afirka da nufin jagorantar aikin doka da oda da a Haiti da ke yankin Caribbean yankin da kungiyoyi dauke da makamai suka haddabi jama’a.

Jami'an tsaro na kokarin tabbatar da tasaro a wasu unguwanin Haiti
Jami'an tsaro na kokarin tabbatar da tasaro a wasu unguwanin Haiti AP - Odelyn Joseph
Talla

 

Shugaban Kenya Ruto ya ce shi da firaministan kasar Haiti Ariel Henry “sun tattauna kan matakai na gaba da za a dauka don ba da damar hanzarta bin diddigin tura sojojin,” amma ba a kai ga bayyana ko yarjejeniyar za ta yi karo da hukuncin da wata kotu ta yanke a watan Janairu da ta bayyana tura sojojin a matsayin “ba bisa ka’ida ba”.

Gwamnatin Haiti ta roki taimakon kasa da kasa don tunkarar tashe tashen hankula da suka yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, yayin da kungiyoyin da ke dauke da makamai suka mamaye sassan kasar baki daya, lamarin da ya bar tattalin arziki da tsarin kiwon lafiyar jama'a cikin tabarbarewa.

Rikici tsakanin yan Sanda da kungiyoyi masu dauke da makamai a Haiti
Rikici tsakanin yan Sanda da kungiyoyi masu dauke da makamai a Haiti REUTERS - Ralph Tedy Erol

A baya dai Kenya ta ce a shirye ta ke ta samar da jami'ai har 1,000, tayin da Amurka da sauran kasashen duniya suka yi maraba da shi, wadanda suka kawar da kai sojojin nasu a kasa.

Sai dai wata kotun Nairobi ta ce matakin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, saboda kasashen biyu ba su rattaba hannu kan wata yarjejeniya ba kan batun.

Wasu daga cikin yan sandan kasar Kenya a Haiti
Wasu daga cikin yan sandan kasar Kenya a Haiti © Tony Karumba / AFP

A ranar Juma'a, Ruto ya ce shi da Henry sun "shaida" yarjejeniyar da aka kulla a Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da aikin na kasa da kasa a farkon watan Oktoba amma hukuncin kotun Kenya ya jefa makomarsa cikin shakku.

Dan siyasar adawa Ekuru Aukot, wanda ya shigar da kara na adawa da tura sojojin, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP a ranar Juma'a cewa zai shigar

Wani mazaunin kasar Haiti ya na mai bayyana damuwa da takaici
Wani mazaunin kasar Haiti ya na mai bayyana damuwa da takaici AP - Odelyn Joseph

Dangane da sukar da ake masa, Shugaban Kenya Ruto ya bayyana matakin na Kenya a matsayin "aiki ga bil'adama", a wani mataki da ya dade yana ba da gudummawa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen waje.

Haiti, wadda ita ce kasa mafi talauci a yammacin duniya, ta shafe shekaru da dama tana cikin tashin hankali, kuma kisan gillar da aka yi wa shugaba Jovenel Moise a shekarar 2021 ya kara jefa kasar cikin rudani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.