Isa ga babban shafi

Rwanda za ta karbi tukuicin dala miliyan 400 gun Birtaniya kan sauke bakin-Haure

Rwanda za ta karbi zunzurutun kudi da ya kai akalla dala miliyan dari 4 da 70 daga Birtaniya a matsayin wani bangare na tukuicin karbar bakin hauren da za a tisa keyarsu zuwa kasar daga Birtaniyar.

Shugaban Rwanda, Paul Kagame.
Shugaban Rwanda, Paul Kagame. © RFI
Talla

Hukumar da ke sa ido a kan yadda gwamnatin Birtaniya  ke kashe kudaden al’umma, wadda ta bayyana haka, ta kuma ce za a biya dala dubu dari da 90 a kan kowane bakon- haure da aka tisa keyarsa zuwa Rwanda a cikin shekaru 5.

Rahoton wannan hukumar na zuwa ne bayan da majalisar dokokin Birtaniya ta yi kira a yi bayani filla-filla a kan kudaden da za a kashe a shirin tisa keyar bakin-hauren.

A watan Janairu, shugaban Rwanda, Paul Kagame ya koka a kan yadda ake daukar lokaci wajen aiwatar da shirin, bayan da caccakar da aka wa shirin ta janyo zanga-zanga, da kuma hukuncin kotu da ya dakatar da shi.

Sai da ma wata kotun koli ta ayyana shirin a matsayin abin da ya saba wa doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.