Isa ga babban shafi

Saliyo za ta hukunta masu satar kasusuwan matattu don yin kayan maye

Mahukuntan Saliyo sun sanar da shirin girke dakaru na musamman don bayar da kariya ga makabartun kasar musamman a Freetown fadar gwamnatin kasar bayan tsannatar fasa kaburbura da sace sassa jikin matattu.

Rahotanni sun ce batagarin na amfani da kasusuwan matattun ne wajen yin wani nau'in kayan maye da ake kira kush.
Rahotanni sun ce batagarin na amfani da kasusuwan matattun ne wajen yin wani nau'in kayan maye da ake kira kush. AP - Andre Penner
Talla

Karkashin dokokin da mahukuntan na Saliyo suka sanya, jami’an gadi na musamman za su bazu a cikin makabartun daga karfe 7 na yammaci har zuwa wayewar garin gobe.

Rahotanni sun bayyana cewa masu fasa kaburburan na cirar kashin matattun ne don hada wani nau’in kayen maye da suke kira kush wanda ke maye gurbin wiwi.

Wani babban jami’I a hukumar da ke kula da makabartu a birnin Freetown da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na AFP da faruwar lamarin inda ya ce galibi barayin kanyi amfani da duhun dare wajen aikata ta’asar.

Duk da cewa AFP ba ta kai ga samun tabbacin hakan daga masu ta’ammali da nau’in kwayar ta kush ba, amma matsalar shaye-shaye na ci gaba da ta’azzara a kasar ta Saliyo da ke yammacin Afrika.

A baya-bayan nan mahukuntan kasar sun tsaurara matakan yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi musamman wiwi wanda ake ganin shi ya assasa matsalar ta fasa makabartun don cirar kashin jikin jama’a.

Wasu majiyoyi sun shaidawa AFP cewa batagarin na nika kashin ne wajen yin kayen mayen wanda ake busawa tare da fita daga hayyaci ko kuma buguwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.