Isa ga babban shafi

Gambia ta kama hanyar soke dokar haramta yi wa mata shayi

Kudurin dokar janye haramta yi wa mata kaciya ya tsallaka zuwa mataki na gaba a Majalisar Dokokin Gambia a jiya Litinin, bayan da mafi rinjayen ‘yan majalisar suka kada kuri’ar tabbatar da hakan.

Sama da mata  miliyan 150 ne aka yi wa kaciya a duniya-UNICEF.
Sama da mata miliyan 150 ne aka yi wa kaciya a duniya-UNICEF. Reuters
Talla

Kudirin soke wannan doka da ta fara aiki tun a shekarar 2015 ya raba kan al’ummar wannan karamar kasar da ke yankin yammacin nahiyar Afrika tsawon watanni, kuma daruruwan mutane ne suka taru a wajen majalisar don nuna adawa shi.

Sai dai ya tabbata cewa masu neman maido da wannan al’ada ta yi wa mata shayi sun fi rinjaye idan aka kwatanta da wadanda suke so a ci gaba da haramta ta, duba da cewa a kuri’ar da aka kada a Majalisar Dokokin Kasar mutane 42 sun goyi bayan kudirin janye haramcin a yayin da 4 suka zabi akasi.

A yayin muhawara kan kudirin dokar, Almameh Gibba, dan majalisar da ya gabatar da kudirin, ya ce makasudin matakin da ya dauka shi ne kare addini da al’adun al’ummarsa, yana mai cewa haramta yi wa mata kaciya, take hakkin al’umma na gudanar da addini da al’adunsu ne.

Da wannan nasara, za a mika kudirin ga wani Kwamitin Majalisar don Nazari a kansa na tsawon watanni 3 kafin ya dawo don karatu na 3.

Wannan batu bai yi wa masu kare hakkin mata dadi da, duba da yadda suke ganin cewa zai bude kofofin dawo da wasu al’adu mara armashi da suka hada da aurar da yara kanana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.