Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Iran ta musanta kai hari kan jiragen daukar mai a mashigin tekun Oman

Kasar Iran tayi watsi da zargin Amurka cewar ita ta kai hari kan wasu jiragen tankunan daukar mai a mashigin tekun Oman, wanda yanzu haka ya haifar da tankiya.

Jirgin ruwan daukar mai da ake zargin Iran ta kaiwa hari a mashigin tekun Oman.
Jirgin ruwan daukar mai da ake zargin Iran ta kaiwa hari a mashigin tekun Oman. ISNA/Handout via REUTERS
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Javad Zarif ya zargi Amurka da gagagwa wajen dora zargin kan Iran ba tare da gabatar da wata shaida da zata tabbatar da hakan ba.

Iran ta kuma bayyana Amurka a matsayin barazana ga zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya da kuma duniya baki daya.

Sai dai Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo yace suna shaidar dake tabbatar da zargin da suke yiwa Iran.

Pompeo ya ce sun samu kwararan shaidu kan zargin

da suke yiwa Iran bayan tatatra bayanan asiri, da kuma nazari kan makamin da akayi amfani da shi, da irin kwarewar da ake bukata wajen amfani da makamin.

Sakataren harkokin wajen na Amurka ya kara da cewa, binciken da suka yi, ya nuna alaka mai karfi tsakanin harin na baya bayan nan, da kuma ire-irensa da Iran ta kai a cikin ‘yan kwanakin nan. Zalika babu kuma wata kungiya dake aiki a yankin dake da kwarewa ko makaman kai irin wadannan hare hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.