Isa ga babban shafi
Czech

Shugabannin Duniya sun yi juyayin mutuwar Vaclav Havel

Shugabannin Kasashen duniya na ci gaba da bayyana alhininsu game da rasuwar Tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Czech, Vaclav Havel, wanda ya jagoranci juyin juya halin kasar.Shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya ce marigayin ya taka rawa wajen gina demokradiyya a Turai, yayin da shugaba Nicolas sarkozy na Faransa, yace Turai ta rasa daya daga cikin fitattun gwarzayenta. 

Gawar Tsohon Shugaban kasar Jamhuriyyar Czech Vaclav Havel inda ake zuwa kai Ziyara kafin binne shi
Gawar Tsohon Shugaban kasar Jamhuriyyar Czech Vaclav Havel inda ake zuwa kai Ziyara kafin binne shi REUTERS/David W Cerny
Talla

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta yaba da rawar da ya taka wajen samun ‘yanci da kuma gina demokradiyya.

A yau Litinin daruruwan ‘Yan kasar ne suka taru a dandalin Prague mahaifar shugaban domin juyayin mutuwarsa.

Havel shi ne shugaban kasar Czechoslovakia tsakanin shekarar 1989 zuwa 1992 kafin kafa Jamhuriyyar Czech inda jagorancin kasar tsakanin 1993 zuwa 2003. Ya mutu yana da shekaru 75 na haihuwa bayan kwashe lokaci yana jinyar cutar ciwon Pneumonia.

Mista Havel ya kwashe Shekaru biyar a kulle a gidan yari. Amma a ranar Lahadi ne Allah ya amshi ransa cikin barcinsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.