Isa ga babban shafi
Yogoslavia-Serbia-Bosnia

Kotu ta wanke Perisic na Yogoslavia daga zargin aikata laifukan yaki

Sashen daukaka kara na kotun hukunta laifukan yaki da aka kafa domin hukunta wadanda ke da hannu a yakin basasar tsohuwar Tarayyar Yougoslavia, ya soke hukuncin dauri na tsawon shekaru 27 da aka yankewa Janar Momcilo Perisic, daga cikin manyan kwamandojin sojan kasar Serbia bayan samunsa da hannu wajen aikata kisan kiyashi a lokacin yaki.

Momcilo Perisic a zauren kotun hukunta laifukan yaki ta Duniya a Yougoslavia
Momcilo Perisic a zauren kotun hukunta laifukan yaki ta Duniya a Yougoslavia REUTERS/Koen Van Weel/ANP/Pool
Talla

Alkalin kotun daukaka karar mai shari’a Theodor Meron ya bukaci a gaggauta sakin Momcilo Perisic wanda yana daya cikin na hannun damar tsohon Shugaban Serbia mai tsatstsauran ra’ayi Slobadan Milosevic daga tsaron da ake yi masa.

Yanke wannan hukunci a kan Persic dan kimanin shekaru 68 a duniya, shi ne kuduri na baya-bayan nan da wannan kotu ta zartas dangane da batun yakin basasa da kuma kisan kiyashin da aka aiwatar a tsohuwar Jamhuriyar Yougoslavia, kisan da aka bayyana shi da a matsayin mafi muni a Nahiyar Turai tun bayan kammala yakin duniya na biyu.

Tsohon kwamandan sojan kasar Yougoslavia, a shekara ta 2011 ne kotun ta same shi da aikata laifuka daban-daban har guda 13, da suka hada da taimakawa Sabiyawan Borsnia domin kashe muslmin a Srebenica, da kuma yi wa birnin Zagreb na kasar Croatia kawanya na tsawon lokaci tsakanin shekarar 1992-1995.

Sai dai a hukuncin da kotun ta yanke a ranar Alhamis, kotun daukaka karar ta bayyana cewa babu cikakkun hujjoji da ke tabbatar da cewa tsohon sojan ya taka rawar da ake cewa ya taka har ma a yanke masa hukuncin dauri na tsawon shekaru 27 a Gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.