Isa ga babban shafi
Amurka

An halatta sayar da tabar wiwi a Colorado a Amurka

Hukumomin Jahar Colorado a kasar Amurka sun bai wa shaguna 348 lasisin damar sayar da tabar wiwi a matsayi Jaha ta farko da ta amince da matakin sayar da tabar a Amurka. Nan gaba ana sa ran wasu Jahohin Amurka zasu bi sahun Colorado a nan gaba.

Ganyen Wiwi a shagunan Jahar Colorado da aka halatta sayar da ganyen tabar a shaguna.
Ganyen Wiwi a shagunan Jahar Colorado da aka halatta sayar da ganyen tabar a shaguna. REUTERS/Rick Wilking
Talla

Daga jiya Laraba a sabuwar shekara ta 2014 ne shagunan suka sami damar sayar da tabar wiwi da nauyinta ya kai akalla gram 28 ga mutanen da shekarun su suka haura 21 a jihar ta Colorado.

Hukumomi a kasar suna hasashen sayar da tabar zai habbaka hanyoyin samar da haraji ga gwamnati da akalla dalar Amurka Miliyan 67 a kowace shekara tare da samar da ayyukan yi da karuwar yawan baki masu yawon bude ido a Jahar.

An bayyana cewa jahar Washington na sahun gaba a jahohin Amurka da za su kaddamar da sayar da tabar a cikin watanni masu zuwa.

Masu karbar haraji sun zura ido domin ganin yadda harkar cinikayyar Tabar za ta habbaka tattalin arziki sakamakon halatta yin amfani da ita a karkashin doka.

Akalla jahohin Amurka 19 ne ke da damar yin amfani da ganyen tabar wiwi domin yin magani, yayin da amincewa da wannan mataki a hukumance ke bai wa al’ummar Jahohin damar shan wannan ganye a wuraren shakatawa ba tare da fuskantar fushin hukuma ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.