Amurka zata rungumi salon diflomasiya-Obama
Shugaba Barack Obama yace kasar Amurka zata rungumi salon diflomasiya sabanin yaki domin warware matsalolinta da kasashen duniya musamman batun mallakar makaman Nukiliya na Iran. A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a zauren Majalisa, Shugaba Obama yace dole Amurka ta canza salo domin tunkarar barazanar da suke fuskanta a wannan zamanin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Obama ya shaidawa Majalisa cewa sun yi kokarin karya shugabancin Kungiyar Al Qaeda amma kungiyar tana da rassa a Yemen da somnalia da Iraqi da Mali.
A cikin jawabinsa, Obama yace zai kalubalanci duk wani kudiri na karfafawa kasar Iran takunkumi domin samun sulhu da kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu