Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka-Rasha

Amurka ta soki shirin jin ra'ayi a Gabashin Ukraine

Kasar Amurka ta soki shirin gudanar da kuri’ar raba gardama da ‘yan a ware ke shirin yi a Gabashin Ukraine, yayin da ake zargin Rasha da hanu a wannan yunkuri domin ta cim ma burinta na mamaye wasu yankunan kasar. 

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kim Hong-Ji
Talla

Hukumomin Ukraine da kasashen yammaci na ganin Rasha na duk iya bakin kokarinta ta ga cewa an gudanar da shirin na raba gardama.

Wannan kuma na faruwa ne a daidai lokacin Rahotanni daga Ukraine, na cewa hukumomin kasar sun kara zage dantse domin ganin sun kwato yankunan wasu garuruwa dake hanun ‘yan aware.

Tun dai a jiya Litinin ne dakarun kasar ta Ukraine suka kara kaimi domin ganin sun murkushe ‘yan aware da suke makale a wasu gine-gine dake garin Slovyansk, wanda shine matattarar rikicin.

Sai dai yayin da hakan ke faruwa, a birnin garin Doneskt, inda aka fara kunna wutar rikicin, hukumomi sun dakatar da tashi da saukar jirage ba tare da an fadi dalilin yin hakan ba.

Yayin da a garin Odessa, inda rikicin ya mamaya a ‘yan kwanakin nan, aka gudanar da jana’izar wadanda suka mutu a wata gobara da ta faru a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sai dai yayin da ake kokarin kwato wuraren daga hanun ‘yan awaren, kasashen yammaci na kokarin ganin cewa an kaucewa fadawa cikin yakin fito na fito, inda yanzu haka Amurka da kungiyar kasashen Turai ke yunkurin tsaurara takunkuman da aka sakawa Rasha, wacce ake zargi da ruruta wutar rikicin kasar ta Ukraine.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.