Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Putin ya lallashi ‘Yan Kishin Rasha a Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bukaci ‘Yan a ware su dakatar da shirin aiwatar da jefa kuri’ar ballewa daga Ukraine tare da bayyana janye dakarun Rasha daga kan iyaka da kasar. Kodayake Ukraine da Amurka suna dari-dari da sabon ikirarin na Rasha.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Alexei Druzhinin/RIA Novosti/Kremlin
Talla

Shugaba Putin na Rasha ya fito yana yin na’am da shirin gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Mayu a Ukraine, bayan a baya Rasha ta fito tana adawa da matakin.

Furucin na Putin a yanzu ana ganin mataki ne mai kyau da zai taimaka a kawo karshe rikicin Ukraine, a yayin da dakarun gwamnatin kasar ke ci gaba fafatawa domin karbe ikon biranen da masu tsananin kishin Rasha suka karbe iko a gabacin Ukraine.

Akwai dai barazanar takunkumi da kasashen Turai da Amurka suke yi wa Rasha idan har aka samu cikas ga zaben na shugaban kasa da aka shirya gudanarwa.

Kuma Duk da cewa Rasha tace dakarunta su fice daga kan iyaka da Ukraine, amma NATO da Amurka suna dari-dari saboda zasu ci gaba da gudanar atisaye a kusa da ukraine

A ranar Lahadi ne ‘Yan a waren Ukraine suka shirya jefa kuri’ar ballewa daga Ukraine zuwa Rasha amma Putin ya nemi su jinkirta, kodayake yanzu babu tabbas ko ‘Yan a waren zasu karbi kiran na shugaban na Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.