Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Hamas na da tasiri a Gaza-Isra’ila

Wani Janar na rundunar Sojan Isra’ila ya ce akwai bukatar barin Hamas ta ci gaba da iko a zirin Gaza, domin abu ne da zai taimaka wajen samar da tsaro a Isra’ila. Manjo Janar Sami Turgeman wanda shi ne babban kwamandan da ke kula da tabbatar da tsaro akan iyakar Gaza da Isra’ila, ya ce duk wani kokarin hana wa Hamas ci gaba da iko a yankin, abu ne dai zai iya cutar da sha’anin tsaron Isra’ila.

Mayakan Kungiyar Hamas a Zirin Gaza
Mayakan Kungiyar Hamas a Zirin Gaza REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

Amma Firaminstan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya daukar Hamas a matsayin kungiyar ‘Yan ta’adda tare da danganta ayyukansu da kungiyar IS da ke da’awar Jihadi a kasashen gabas ta tsakiya.

A bara Isra’ila ta shafe kwanaki 50 tana fada da Hamas a Zirin Gaza, rikicin da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 2,200 da Yahudawan Isra’ila 71.

Kwamandan Sojan ya ce idan dai za a sa tsaro a kan gaba, to Hamas na da matukar tasiri a zirin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.