Isa ga babban shafi
Amnesty

Amnesty za ta kada kuri’ar amincewa da halaccin Karuwanci

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International za ta kada kuri’ar amincewa da bukatar halatta karuwanci a duniya a matsayin kare hakkin bil’adama a taron da ta ke gudanarwa yanzu haka a Dublin.

Mata na tsallakawa zuwa Italiya domin yin karuwanci
Mata na tsallakawa zuwa Italiya domin yin karuwanci Photo Grain Media
Talla

Ana sa ran wakilan kungiyar da ke halartar taron daga sassan kasashen duniya za su jefa kuri’ar hallatawa ko haramtawa a matsayin hakkin Bil Adama.

Amnesty na ganin sana’ar Karuwanci zabi ne na rayuwa da mata suka sa kansu domin samun kudi.

Sai dai wasu na ganin akwai matsaloli da dama da ke jefa Mata shiga Karuwanci da ya kamata ace Amnesty ta yi yaki da su, da suka hada da Fyade da fataucin Mata domin tursasa ma su shiga Karuwanci.

A karshen makon da ya gabata kungiyar karuwan Najeriya ta gudanar da taronta a Lagos, inda aka samu rikici wajen zaben wadanda za su jagoranci Karuwan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.