Isa ga babban shafi
ICC-Congo

An soma Shari’ar Ntaganda a Kotun ICC

An soma shariar madugun ‘yan tawayen kasar Jamhuriyyar Congo Bosco Ntaganda da ake kira Terminator, a kotun hukunta masu aikata manyan laifukan yaki da ke Hague. Ana zargin sa ne da aikata kazaman ayyukan yaki da suka hada da yi kananan yara fyade, tare da tusasawa kananan yara shiga aikin soja.

Shugaban 'Yan tawayen Congo Bosco Ntaganda
Shugaban 'Yan tawayen Congo Bosco Ntaganda Reuters
Talla

Babbar mai shigar da kara a kotun Fatou Bensouda ta fadi cewa kotun na tuhumar Ntaganda da tursasawa kananan yara rungumar makamai da cusa masu ra’ayoyi marasa kyau.

Kotun na tuhumarsa da aikata munanan laifukan yaki 18.

Kuma a zaman kotun a yau za a gabatar da shaidu 80 kan hare haren da aka kai wa fararen hula a lardin Ituri a Jamhuriyar Congo tsakanin 2002 zuwa 2003.

Rikicin ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin 60,000.

A 2013 ne Bosco Ntaganda ya mika kan shi a ofishin jekadancin Amurka a Kigali kasar Rwanda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.