Isa ga babban shafi
ICC-Congo

Kotun ICC za ta fara shari’ar Ntaganda a ranar Laraba

Kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya tace zata fara shari’ar tsohon shugaban ‘yan tawayen Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo, Bosco Ntaganda da ake kira The Terminator ranar laraba mai zuwa kan zargin da ake masa na fyade ga yara da tursasawa yara daukar makamai.

Shugaban 'Yan tawayen Congo Bosco Ntaganda
Shugaban 'Yan tawayen Congo Bosco Ntaganda REUTERS/Toussaint Kluiters/United Photos/Pool
Talla

Kotun ta ce alkali Robert Fremr zai bude shari’ar a Hague a ranar Laraba inda ake tuhumar Ntaganda da laifufukan yaki 13 da kuma wasu 5 na cin zarafin Bil Adama.

Kafin soma sharia’ar, Babbar mai gabatar da kara a kotun ICC Fatou Bensouda za ta fara gabatar da jawabi kafin lauyan da ke kare Ntaganda da kuma wadanda ke wakiltar mutane 2,149 da al’amarin ya shafa.

Ntaganda dai ya taka rawa wajen kashe mutane 60,000 a yakin kasar Congo da aka fara a shekarar 1999.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.