Amruka da China sun amince su yaki masu kutsen shafukan Internet tare
Shugaban kasar Amruka Barak Obama da ya gana a fadarsa ta Wait House da takwaransa na kasar china Xi Jimping a ranar jiya juma’a 25 ga watan Satumba 2015, a ziyarar da shugaban kasar ta Chana ya kai a karo na farko a kasar Amruka, ya ce sun cimma yarjejeniyar yaki da matsalar kutse ta yanar Internet a tsakanin kasashen nasu 2
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ita dai wannan ziyara da shugaban na China ya kai a Amruka, ta zo ne a dai dai lokacin da ake tada jijiyoyin wuya tsakanin kasashen 2, kan halayyen da China ke nunawa a mashigan ruwanta, da kuma zargin taka rawa a badakalar satar bayanan sirin ta Internet, da ya shafi wasu kamfanoni da ma’aikatun gwamnatin kasar Amruka
Tuni dai a nasa bangaren shugaban kasar China Xi Jimping ya mayar da martini kan zargin kasarsa da hanna jiragen ruwan kasashen duniya karakaina a gabar tsibiran dake mallakin kasar ta China, inda ya ce mallakin kasar ne kuma tana da ikon tsare gabobin ruwanta kamar ko wace iyaka da take da ita ta kasa
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu