Blair ya sake neman afuwa akan mamayar Iraqi
Tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair ya nemi gafara kan mamayar da suka yi wa kasar Iraqi da kuma kashe shugabanta Saddam Hussein a shekarar 2003, tare da danganta mamayar da haifar da mayakan IS da suka kwace ikon wasu yankunan Iraqi da Syria.
Wallafawa ranar:
Sai dai Blair ya ce bai yi nadamar kawar da Saddam Hussian ba, amma ya nemi afuwa akan kuskurensu daga bayanan sirin da suka samu.
Blair ya amince da cewar mamayar da suka kai kasar ce ta haifar da mayakan ISIS a yau, wadanda suka zama barazana ga duniya baki daya.
A bayanan tosohon Firimiyan na Britaniya da aka wallafa a shafin kafar yada labarai ta CNN ya ce akwai kamshin gaskiya akan alakar mamayar da Amurka da Birtaniya suka yi wa Iraqi da kuma samuwar mayakan IS.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu