Isa ga babban shafi
Brazil

Zanga-zangar tsige Rouseff daga Shugabanci a Brazil

Dubban Al’ummar Brazil ke gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban na kasar, Inda suka bukaci shugabar kasar Dilma Rouseff ta sauka daga kujerar ta adai-dai lokacin da kasar ke fuskantar tabarbarewar tattalin arziki.  

Zanga-zanga a Brazil
Zanga-zanga a Brazil REUTERS
Talla

Rouseff wadda ke kokarin kare mutuncinta ta fannin siyasa na fuskantar zarge-zarge a game da sauya tsarin kasafin kudin shekara na kasar yayin da ta ce, gwamantocin da suka shude suma tsarin suka bi.

Jami’an ‘yan sanda sun ce kimanin mutane dubu 83 ne suka bazama a birane 87 na kasar domin zanga zangar,  sai dai jagororin ‘yan adawa sun musanta batun, inda suka ce adadin mutanen ya haura dubu 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.