Mexico ta sake cafke Chapo Guzman
Hukumomin Mexico sun sake cafko Joaquin da ake kira El Chapo Guzman watanni shida bayan ya sulale a wani babban gidan yarin da ake tsare da shi.
Wallafawa ranar:
El Chapo wanda babban shugaban masu fataucin miyagun kwayoyi ne da ake nema ruwa a jallo, ya haka rami ne a gidan yarin ya sulale a ranar 11 ga watan Yuli, al’amarin da ya zama babban kalubale ga shugabar Mexico Enrique Pena Nieto.
A shafin shi na Twitter shugaban na Mexico ya ce gurinsu ya cika domin sun cafko shi.
Akwai dai hutunan shi da ake ta yadawa a Intanet bayan an kamo shi sanye da wata bakar riga a yankin Sinaloa.
Yanzu haka kuma rahotanni sun ce an kama hanyar mayar da shi gidan yarin Altiplano da ya sulale.
Sai dai kuma El Chapo ya shattserewa a gidan yarin da ake tsare da shi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu