Isa ga babban shafi
EU-Turkiya

EU ta cimma matsaya kan 'yan gudun hijira

Shugabannin kasashen Turai sun cimma matsaya wadda za a gabatar wa Turkyiya domin kai ga cimma yarjejniyar magance matsalar kwararar ‘yan gudun hijira.

'Yan gudun hijirar da ke namen mafaka a kasashen Turai
'Yan gudun hijirar da ke namen mafaka a kasashen Turai Reuters
Talla

Firaminsitan Luxembourg, Xavier Bettel ya ce, a safiyar yau jumma’a za a gabatar da matsayar ga Firaministan Turkiyya Ahmet Davutoglu .

Matsayar dai za ta bukaci a maido da ‘yan gudun hijirar da ke kaura dagaTurkiya zuwa Girka yayin da ake tsammanin kungiuyar Tarayyar Turai za ta bai wa Turkiyyan tallafin kudade da tare da sanya ta cikin jerin kasashe masu bisar kawance ta zirga zirga tasakanin tarayyar Turai.

Har ila matsayar ta kunshi cewa, duk wani dan gudun hijirar Syria da aka mayar, Turai za ta karbi wani dan gudun hijirar Syria daban daga sansanin Turkiya domin ba shi matsugunni.

Tun lokacin yakin duniya na biyu, raban da a samu gagarumar matsalar kwararar 'yan gudun hijira irin ta wannan lokacin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.