Isa ga babban shafi
Amnesty

Hukuncin kisa a duniya ya karu- Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty Intarnational ta ce, an samu karuwar zartar da hukuncin kisa da sama da kashi 50 a fadin duniya a bara kawai, wanda shi ne adadi mafi girma tun a shekarar 1989.

Amnesty ta ce hukuncin kisa ya karu da kashi 50 a wasu kasashen duniya  a bara
Amnesty ta ce hukuncin kisa ya karu da kashi 50 a wasu kasashen duniya a bara Getty Images/Volkan Kurt
Talla

A cikin rahoton na Amnety da ta fitar a wannan Laraba ta ce, adadin mutane 1,634 aka zartar wa hukuncin kisa a shekarar 2015 da ta gabata.

kuma rahoton ya ce wannan shi ne adadi mafi girma a tsawon shekaru 27 yayin da kasar Iran ke sahun gaba da Pakistan da Saudiya Arebiya.

Akalla mutane 977 Iran ta zartarwa hukuncin kisa a cewar rahoton, Pakistan kuma mutane 326, a saudiya kuma 158 dukkaninsu a shekarar da ta gabata.

Amnesty ta ce, yawancin wadanda aka kashe a Saudiya baki ne wadanda ba su fahimtar harshen larabci.

Sai dai adadin bai shafi kasar China ba da rahoton na Amnesty ya ce dubbai ne gwamnatin kasar ta zartarwa hukuncin kisa.

Ana zartar wa mutane da hukuncin kisa kan laifukan da suka shafi kisa da safarar miyagun kwayu da fashi da makami da ridda da garkuwa da mutane da fyade da kuma wadanda suka ci mutuncin addinin Islama a kasashen musulmi.

Rahoton na Amnesty ya bukaci a kawo karshen kisan mutane kamar yadda wasu kasashe suka soke dokar hukuncin kisa a kundin tsarin mulkinsu.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.