An Aiwatar da Hukuncin Kisa kan Mutane 70 a Saudiyya
Kasar Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa kan wani mutun na 70 a cikin wannan shekara da ake zartas da hukunci kan su saboda aikata manyan laifuka.
Wallafawa ranar:
An zargi Alaa al-Zahrani da laifin kashe wani dan Saudiyya Abdullah al-Sumairi ta hanyar kwankwantsa kai da wani katon gungumen dutse.
Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ya ce a tsawon shekarar data gabata an kashe mutane 153 ne saboda aikata laifuka da suka hada da fataucin miyagun kwayoyi, fashi da makami da sauran laifuka da aka haramta.
A cewar Kungiyar Amnesty ta duniya shekara ta 2015 ta fi kowace shekara, cikin shekaru 20, da aka fi samun yawan masu laifuka da aka kashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu