Isa ga babban shafi
Syria

Ana azabtar da mutane a gidajen yarin Syria -Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi zargin cewar hukumomin Syria na azabtar da mutane a gidajen yarin kasar. Wannan kuma na zuwa ne a yayin da Amurka da Rasha ke cacar-baki kan yadda Rasha ke amfani da kasar Iran wajen kai harin sama cikin Syria.

Shugaban Syria Bashar al Assad
Shugaban Syria Bashar al Assad REUTERS
Talla

Rahotan da kungiyar Amnesty International ta fitar ya nuna cewar hukumomin Syria na cin zarafin mutanen da ake tsare da su ta hanyar duka da sanya ma su wayar wutar lantarki a jiki da fyade da kuma wasu laifufuka da ke da nasaba da cin zarafin Bil Adama.

Kungiyar ta ce duk wanda aka ga alamar cewar yana adawa da gwamnatin kasar, ya kan fuskanci cin zarafin da ya hada da tsarewa da azabtarwa da ma kisa wani lokacin.

Kungiyar ta ce ta samu bayanan ne bayan tattaunawar da ta yi da mutane 65 da aka ci zarafinsu kuma akasarin su fararen hula ne wadanda suka tabbatar da labarin a Cibiyar tsaro da kuma gidan yarin soji da ke Saydnaya.

Rahotan ya ce mutane sama da 17,700 ake hasashen sun mutu lokacin da ake tsare da su a gidan yarin kasar tun fara yakin da aka yi a shekarar 2011 wanda ke nuna cewar mutane 300 ke mutuwa duk wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.