Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

MDD za ta sanya takunkumi kan Koriya ta Arewa

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shirin kakaba jerin takunkumai kan Koriya ta Arewa bayan ta yi gwajin makamin Nukilya a karo na biyar, abinda ya haifar da cece-kuce a kasashen duniya.

Gwajin da Koriya ta Arewa ta yi ya janyo cece-kuce a kasashen duniya
Gwajin da Koriya ta Arewa ta yi ya janyo cece-kuce a kasashen duniya REUTERS/KCNA
Talla

Kwamitin ya shaida wa manema labarai cewa, zai dauki wannan matakin kan Koriya ta Arewa kamar yadda sashi na 41 a kundin dokokin Majalisar Dinkin Duniya ya shata.

Kasashen Koriya ta Kudu da Amurka da Japan da Rasha da China, duk sun caccaki gwajin makamin na Nukiliya wanda karfinsa ya kai maki 5 da rabi.

Ko a shekarar 2006, sai da Majalissar Dinkin Duniya ta sanya jerin takunkumai har biyar kan Koriya ta Arewa saboda gwajin makamin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.