Isa ga babban shafi
Turkiya-|ran

Iran ta gana da Turkiya kan rikicin Syria

Ministan harkokin wajen Iran, Mohammed Javad Zarif na ziyara a birnin Ankara na Turkiya a wannan Laraba don ganawa da takwaransa, Mevult Cavusoglu kan rikicin Syria. 

Ministan harkokin wajen Iran, Mohammed Javad Zarifa da takwaransa na Turkiya, Mevlut Cavusoglu
Ministan harkokin wajen Iran, Mohammed Javad Zarifa da takwaransa na Turkiya, Mevlut Cavusoglu REUTERS/Stringer
Talla

A karo na uku kenan cikin kasa da watanni biyu da Mr. Zarif ke gudanar da irin wannan tattaunawar da mahukuntan Tukiya.

Baya ga rikicin na Syria, har ila yau, Mr. Zarif wanda ya yada zango a Turkiya daga birnin New York na Amurka, in da ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya, ya tattauna da takwaransa, Mevlut Cavusoglu kan wasu batutu da suka shafi huldar kasashen biyu.

Kasashen dai nada sabanin ra’ayi kan rikicin Syria, in da Iran ke goyon bayan gwamnatin Bashar al- Assad, yayin da Turkiya ke mara wa ‘yan tawayen da ke kokarin kifar da gwamnatinsa, sannan kuma ta kaddamar da aikin soji a Syria da nufin kakkabe kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka hada mayakan ISIS.

Duk da wannan sabanin da ke tsakaninsu game da rikicin na Syria, kasashen biyu sun yi aiki tukuru a ‘yan watannin da suka shude don karfafa dangantarsu.

Wani lokaci a yau ne kuma, Mr. Zarif zai gana da da Firaministan Turkiya, Binali Yildrim.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.